Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-31 19:43:16    
Kasashen duniya sun ci gaba da ba da taimako ga yankunan girgizar kasa na Sin

cri

A ran 31 ga watan Mayu, Kungiyar ba da agaji ta Red Crescent Societies ta kasar Pakistan ta bayar da tantuna dubu 3 ga yankunan da ke fama da girgizar kasa na Sin ta ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Pakistan. Kai tsaye ne, za a yi jigilar wadannan tantuna da jiragen sama daga birnin Islamabad zuwa yankunan da suke fi shan wahalar girgizar kasa na lardin Sichuan.

A ran 30 ga watan Mayu, babban sakataren majalisar ministocin kasar Japan Mr. Machimura Nobutaka ya sanar da cewa, gwamnatin kasar Japan za ta bayar da karin taimakon kudi da yawansu ya kai kudin Japan Yen miliyan 500 ga yankunan girgizar kasa na Sichuan. Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Mr. Qin Gang ya bayyana a wannan rana da dare cewa, gwamnatin kasar Sin ta yi maraba da hakan da kuma nuna godiya ga gwamnatin kasar Japan.

A halin yanzu dai, bi da bi ne, aka yi jigilar tantunan da kasashen Masar, da Faransa, da Ukraine, da Belarus da suka bayar ga kasar Sin zuwa birnin Chengdu na lardin Sichuan.(Danladi)