"Kasar Sin wata kasa ce da ke samun cigaba, kuma abokiya ce ta kasashen Afirka. Na amince da cewa kasar Sin za ta iya cin nasarar fama da wannan babbar bala'in girgizar kasa mai tsanani sosai". Mr. Eleih-Elle Etian, jakadan kasar Kamaru da ke nan kasar Sin kuma shugaban kungiyar jakadun kasashen Afirka da ke nan kasar Sin ya fadi haka ne a gun wata liyafar da ya shirya domin taya murnar "Ranar kasar Kamaru" kafin ya bar mukaminsa na jakadan kasar Kamaru a nan kasar Sin.
Mr. Eleih-Elle Etian ya ce, a cikin shekaru 19 da suka wuce lokacin da yake aiki a nan kasar Sin a matsayin wani dan diplomasiyya, ya ga yadda kasar Sin ta samu cigaba da idonsa. Sabo da haka, yana kaunar kyakkyawar kasar Sin wadda take da girma kwarai, kuma ya amince da cewa, tabbas ne kasar Sin za ta iya cin nasarar fama da bala'in girgizar kasa mai tsanani.
Mr. Zhang Yesui, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin ya bayyana wa mahalarta yadda jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnati da jama'a na kasar Sin suke fama da bala'in. Ya kuma nuna godiya ga jakada Eleih-Elle Etian domin gudummowar da ya bayar wajen ciyar da dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka gaba.
Mr. Li Zhaoxing, tsohon ministan harkokin waje na kasar Sin, kuma shugaban kwamitin kula da harkokin waje na majalisar dokokin kasar Sin ya kuma halarci wannan liyafa.
Kafin a kaddamar da liyafar, mahalarta sun nuna jimami na tsawon minti guda ga mutanen da suka mutu sakamakon bala'in girgizar kasa da ya auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan. (Sanusi Chen)
|