Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-30 18:27:09    
Kasar Sin tana yin namijin kokarinta wajen gina gidaje na wucin gadi domin mutanen da suke fama da bala'in girgizar kasa

cri
Kasar Sin tana yin namijin kokarinta wajen gina gidaje na wucin gadi domin mutane fiye da miliyan 5 da suka rasa gidajensu a sakamakon bala'in girgizar kasa da aka samu a lardin Sichuan.

Masana sun ce, kafin a kammala aikin sake raya yankuna masu fama da bala'in, wadannan mutane za su yi shekaru 3 zuwa shekaru 5 suna zama a cikin wadannan gidaje na wucin gadi.

Bisa shirin da ma'aikatar gidaje da raya birane da kauyuka ta kasar Sin ta tsara, za a kammala aikin kera gidaje na wucin gadi miliyan 1 cikin watanni 3 masu zuwa. An tabbatar da cewa, wadannan gidaje na wucin gadi za su iya fama da bala'in girgizar kasa da zafi, kuma za a iya yin amfani da su har shekaru 3 zuwa shekaru 5.

Yanzu, larduna fiye da 20 na kasar Sin suna gaggauta kera wadannan gidaje na wucin gadi miliyan 1, kuma ana sufurinsu zuwa yankunan lardin Sichuan da ke fama da bala'in girgizar kasa. (Sanusi Chen)