Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-30 17:00:05    
Lin Li ta sake samun goguwa a wasannin Olympics

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, a duk tsawon lokacin da ake yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing, aka fi mayar da hankali kan mai daukar fitilar wasannin na farko na kowane zango kan hanyar yawo da fitilar wasannin, wanda kuma ka iya wakiltar mutane dake da halayen musamman na zangon. A birnin San Francisco na kasar Amurka, mai daukar wutar yula ta farko ta gasar wasannin Olympics ta Beijing ita ce Madam Lin Li, sannanniyar tsohuwar 'yan wasan iyo ta kasar Sin. Tana mai cewa: 'Lallai na yi alfahari da samun damar mika fitilar wasannin Olympics. Amma na firgita a zuciyata kwanaki biyu kafin a sanar da ni a matsayin mai daular fitilar wasannin na farko'.

Aminai 'yan Afrika, ko kun manta da ita ? Ashe, ita ce wata zakara ta farko ta wasan iyo na duniya a kasar Sin. Sunanta Lin Li, wadda ta taba shiga gasannin Olympics har sau uku a jere. Kuma ta sami lambar zinariya ta wasan iyo mai salo daban-daban tsakanin mace da mace na tsawon mita 200 a gun wasannin Olympics na Barcerona da aka gudanar a shekarar 1992 a birnin Barcerona na kasar Spain. Ko da ta sami lambar azurfa a gasar wasannin Olympics, ita Madam Lin Li ta ba mutane mamaki kwarai da gaske. Yanzu dai, shekarunta sun kai 38 da haihuwa.

Jama'a masu saurare, shekaru 12 ke nan da Madam Lin Li ta janye daga dandalin wasan iya bayan gasar wasannin Olympics ta Atlanta a shekarar 1996. Ta fada wa wakilinmu cewa : "Bayan gasar wasannin Olympics ta Atlanta a shekarar 1996, na taba zama mai koyar da 'yan wasa na tsawon shekaru biyu a yankin Hongkong. Daga baya dai, na sake koma wa lardin Jiangsu na kasar mahaifa domin yin aikin koyarwa. Bayan wannan lokaci dai, na zo nan kasar Amurka domin koyon harshen Turanci. Amma burina bai tabbatu ba sakamakon wassu sauye-sauyen lamura. Hakan ya sa ni zuwa wani club din wasannin iyo domin yin aikin koyarwa na tsawon shekaru uku zuwa hudu, inda na yi aure sa'annan na samu 'ya'' .

Mijin Madam Lin Li, shi ma wani Basine ne, wanda ya je kasar Amurka daga kasar Sin domin yin aikin kula da harkokin kudi. Lin Li ta ce, yanzu ta rigaya ta fi mayar da hankali kan zaman iyalinta yayin da take kashe wassu lokuta wajen koyar da 'yan wasan iyo a wani club din wasan iyo na kasar Amurka. Ta kuma tabbatar da cewa, ko ta yaya ba za ta manta da tarihinta na wasannin motsa jiki a matsayin wata zakarar wasannin Olympics ba.

Samun damar daukar wutar yola ta wasannin Olympics da Madam Lin Li ta yi a wannan gami lallai ya sosa zuciyarta kwarai da gaske. Tana mai cewa : ' Na ji kamar na sake samo abubuwa masu dadi dake kasancewa cikin zuciyata yayin da nake shiga gasar wasannin Olympics a wancan lokaci. Ina so in fadi cewa, in Allah ya sake mayar da ni a matsayin matashiya, to zan so a ce na shiga gasar wasannin Olympics ta Beijing'.

Lallai wasa ne Madam Lin Li ta yi na sake shiga gasar wasannin Olympics. Daya daga cikin manufofin rayuwarta na yanzu ita ce, taka rawar a-zo-a-gani wajen daukar nauyin mama a wuyanta.

Wassu mutanen da abin ya shafa sun ce, dalilan da suka sa aka zabi Madam Lin Li a matsayin mai dauke da fitilar wasannin Olympics ta farko a birnin San Francisco, su ne: ta taba samun lambar zinariya a gun gasar wasannin Olympics; kuma ita wata Basiniya ce da ka iya wakiltar Sinawa dake zaune a unguwoyin birnin, wadanda suka bada babban taimako ga raya birnin na San Francisco. ( Sani Wang )