Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-29 20:43:11    
Mutane 68516 sun mutu sakamakon girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan

cri
A ran 29 ga wata da yamma, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ba da labari bisa umurnin babban ofishin ba da umurni kan fama da girgizar kasa da gudanar da ayyukan ceto na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, cewa ya zuwa ran 29 ga wata da safe da karfe 12, girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin ya riga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 68516 yayin da mutane fiye da dubu 360 suka jikata, kuma mutane fiye da 19300 suka bace, ban da wannan kuma an riga an kaurar da mutane da kuma tsugunar da su fiye da miliyan 15. Yawan mutanen da ke fama da bala'in ya kai fiye da miliyan 45.5.

Ya zuwa ran 28 ga wata da dare da karfe 12, an riga an ceci mutane da kuma kaurar da su kusan dubu 740, da kuma kubutad da mutane 6541 daga kangaye.

Ban da wannan kuma ya zuwa ran 29 ga wata da safe da karfe 12, yawan mutanen da suka samu jiyya a cikin asibitoci domin jin rauni a cikin girgizar kasa ya kai kusan dubu 87, kuma a ciki an sallame su dubu 56 daga asibitocin, haka kuma birnin Chongqing da dai sauran larduna 20 sun karbi 'yan lardin Sichuan masu jin raunuka 7659.

Bugu da kari kuma ya zuwa ran 29 ga wata da safe da karfe 12, gwamnatoci na matakai daban daban na kasar Sin sun kebe kudaden Sin Yuan biliyan 21 wajen fama da girgizar kasa, yawan kudade da kayayyakin taimako da kasar Sin ta samu daga gida da waje ya kai Yuan biliyan 37.3.(Kande Gao)