Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-29 19:36:03    
Kafofin watsa labaru na kasashen duniya suna ganin cewa Sinawa na hadin kansu sosai domin fama da bala'i

cri

Ran 28 ga wata, wasu kafofin watsa labaru na kasashen duniya suna cigaba da lura da bala'in babbar girgizar kasa da ya faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, kuma sun yabawa ayyukan tinkarar bala'in da kasar Sin ke gudanarwa da rahotannin da kafofin watsa labaru na kasar Sin suka yi bisa yadda abubuwan suka kasance, kuma suna ganin cewa, aikin fama da bala'in ya kara hada kan Sinawa sosai.

Jaridar "Sin Chew Jit Poh" ta kasar Malaysiya ta ba da sharhi cewa, yayin da ake fuskantar da matsanancin bala'in girgizar kasa, gwamnatin kasar Sin ta yi iyakacin kokari domin taimakawa mutanen da suke fama da bala'in, kuma ana hada kan dukkan Sinawa tamkar tsintsiya madauniki daya.

Jaridar "Chinese Biz News" ta birnin Los Angeles na kasar Amurka ta bayar da bayanin edita domin yabawa gwamnati da jama'ar kasar Sin sun nuna sabon ainihin zaman al'umma ta hanyar gudanar da ayyukan fama da bala'in. Kuma an bunkasa tunanin "mai da mutum a matsayi mafi muhimmanci" da gwamnatin kasar Sin take tafiya sosai.