Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-23 22:00:09    
Ba a sami manyan matsalolin da girgizar kasar ta haifar wa muhalli ba

cri
Yau a nan birnin Beijing, mataimakin ministan muhalli na kasar Sin, Mr.Wu Xiaoqing ya bayyana cewa, har zuwa yanzu, ba a sami manyan matsalolin da girgizar kasa ta haifar wa muhalli ba.

A gun taron manema labarai da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya kira, Mr.Wu Xiaoqing ya ce, bayan aukuwar girgizar kasar, sassan muhalli sun mayar da samar da ruwan sha mai inganci ga yankunan da girgizar kasar ta shafa a matsayi na farko, kuma sun fara binciken muhalli daga dukan fannoni. A sa'i daya kuma, sassan muhalli sun gudanar da bincike a kan yankunan da girgizar kasa ta shafa, don tabbatar da tsaron na'urorin nukiliya.

Bayan haka, a cewar Mr.Wu Xiaoqing, ya zuwa ran 22 ga wata, ruwan da aka samu daga mafarin ruwa da ke yankunan da girgizar kasa ta shafa a lardin Sichuan da garuruwan da ke makwabtaka da su ya dace da ma'aunin da aka tsai da.(Lubabatu)