Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-23 20:34:39    
mutane 55740 sun rasu sakamakon girgizar kasa da ta afka wa gumdumar Wenchuan

cri
Ya zuwa yau 23 ga wata da karfe 12, yawan mutanen da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon girgizar kasa mai tsanani da ta afkawa gumdumar Wenchuan ta lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, ya riga ya kai 55,740, kuma an sake tsugunar da jama'ar da yawansu ya kai fiye da miliyan 11 da dubu 360.

Labarin da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar a yau 23 ga wata ya yi nuni da cewa, ya zuwa ran 23 ga wata da karfe 12, girgizar kasar ta riga ta jikkata mutanen da yawansu ya kai sama da dubu 290, a yayin da wasu 24,960 suka bace sakamakon girgizar. Bayan haka, kudade da kayayyakin agaji da aka bayar a gida da kuma waje sun riga sun wuce kudin Sin yuan biliyan 24 da miliyan 600.(Lubabatu)