Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-23 20:27:06    
Darajar taimakon da wasu kungiyoyin kasashen duniya da kasashe suka bayar cikin gaggawa kan girgizar kasa da ta auku a lardin Sichuan, ta kai dalar Amurka miliyan 20.55

cri
Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta gabatar da cewa, ya zuwa ranar 23 ga wata da karfe 10, darajar taimakon da kungiyoyin kasashen duniya da kasashen da abin ya shafa suka bayar cikin gaggawa kan yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, ta kai dalar Amurka miliyan 20.55.

A 'yan kwanakin da suka wuce, kasashen Australia, da Italy, da Cuba, da hukumar raya kasa ta duniya ta kasar Amurka, wato USAID, da kasar Turkmenistan, da dai sauransu, daya bayan daya ne suka bayar da taimako a fannonin kudi, da kayayyaki, da na aikin likitanci ga yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan. (Bilkisu)