Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-23 19:51:20    
Gamayyar kasa da kasa tana ci gaba da ba da taimako ga yankunan girgizar kasa na Sin

cri

A ran 22 ga wata, gamayyar kasa da kasa tana ci gaba da ba da taimakon kudi da kayayyaki ga yankunan girgizar kasa na lardin Sichuan na kasar Sin, domin taka rawa wajen yaki da girgizar kasa da sake gina yankunan bayan bala'in girgizar kasa.

Jiya da safe, kayayyakin agajin da darajarsu ta kai dala dubu 815 da hukumar USAID ta sake baiwa mutanen da bala'in girgizar kasa ya rutsa da su suka isa birnin Chengdu na lardin Sichuan, ciki har da na'urorin bidar mutane, da na ceto da warkar da mutane wadanda suka ji rauni

A waje daya kuma, kayayyakin agaji da kasar Turkmenistan ta baiwa yankunan da bala'in girgizar kasa ya shafa sun isa filin jirgin sama na Zhongchuan dake birnin Lanzhou na lardin Gansu jiya 22 ga wata da dare. Nauyin kayayyakin ya kai ton 23 gaba daya, ciki har da kayan sutura, barguna, da matashin kai, magunguna, da dai sauran na'urorin aikin jiyya, wadanda ake bukatarsu ruwa a jallo a yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su.

Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Argentina ta sanar da cewa, kasar ta riga ta yi jigilar kayayyakin agaji na karo na farko zuwa kasar Sin, cikin har da tankuna da ake iya zama a waje da yawansu ya kai 40 da kuma manyan tankuna 5. Haka kuma an riga an shirya taimakon agaji na jin kai na karo na biyu. Kasashen Jamus da Pakistan da Australiya da Mauritania su ma sun bayar da taimakon kudi da kayayyaki ga kasar Sin.(Danladi)