Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-23 12:00:45    
Manyan jami'an kamfanonin jarin waje na birnin ChengDu sun yaba wa kokarin da gwamnatin kasar Sin da jama'arsu suka yi yayin da suka yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane

cri
Ran 22 ga wata, yayin da manyan jami'an kamfanonin jarin waje da ke unguwar raya fasahar koli ta zamani a birnin Chengdu suke zantawa da manema labaru na CRI, bi da bi ne suka yaba wa kokarin da gwamnatin kasar Sin da jama'arsu suka yi wajen yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane.

Mataimakin babban jami'i mai zartaswa na kamfanin sadarwa na Ericsson na kasar Sin kuma basinnen da ke kasar Malaysia Lin Qingwen ya bayyana cewa, matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka wajen yaki da girgizar kasa da ceton mutane ya burge ni sosai. Ban taba ji ko wane basinne da ya yi koke-koke ga gwamnati ba, sabo da haka suka gamsu da kokarin da gwamnati ta yi wajen bayyana halin da bala'in girgiza ke ciki da yaki da girgizar kasa da ceton mutane.

Manaja na kamfanin sadarwa ta kimiyya da fasaha ta Singapore, William Gan Kian Hock ya bayyana cewa, matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka ta yi kyau kuma tana da amfani sosai, kowa da kowa za su iya ganin abubuwan da suka faru. Jaridar kasashen waje sun bayar da labari game da matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka cikin lokaci, kuma ya yi baban tasiri a duniya.(Bako)