Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-23 11:34:50    
Hukumar USAID ta Amurka, da kasashen Turkmenistan da Rasha sun bayarwa yankunan da bala'in girgizar kasa ya shafa a kasar Sin kayan agaji da aikin jinya

cri
Jiya 22 ga wata, hukumar Amurka mai kula da harkokin raya kasashen duniya wato USAID, da kasashen Turkmenistan da Rasha suka cigaba da bayar da kayayyakin agaji da aikin jinya ga yankunan kasar Sin da mummunan bala'in girgizar kasa ya rutsa da su.

Jiya da safe, kayayyakin agajin da darajarsu ta kai dala dubu 815 da hukumar USAID ta sake baiwa mutanen da bala'in girgizar kasa ya rutsa da su suka isa birnin Chengdu na lardin Sichuan, ciki har da na'urorin bidar mutane, da na ceto da warkar da mutane wadanda suka ji rauni

A waje daya kuma, kayayyakin agaji da kasar Turkmenistan ta baiwa yankunan da bala'in girgizar kasa ya shafa sun isa filin jirgin sama na Zhongchuan dake birnin Lanzhou na lardin Gansu jiya 22 ga wata da dare. Nauyin kayayyakin ya kai ton 23 gaba daya, ciki har da kayan sutura, barguna, da matashin kai, magunguna, da dai sauran na'urorin aikin jiyya, wadanda ake bukatarsu ruwa a jallo a yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su.

Ya zuwa jiya da tsakiyar rana, yawan mutanen da suka ji rauni wadanda ake yi musu jinya a asbitin tafi-da-gidanka na Rasha ya riga ya kai 47.(Murtala)