Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-23 10:59:04    
Jaridar People's daily ta ba da bayyani cewa kasar Sin ta nuna godiya ga dukkan duniya da suka bayar da gudummawa marasa son kai ga yankunan da aka yi girgizar kasa a lardin Sichuan a kasar Sin

cri
Ran 23 ga wata, jaridar People's Daily da ake bugawa a nan birnin Beijing ta ba da bayyani cewa, yayin da mutanen kasar Sin suka yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane, gudummawa marasa son kai daga dukkan al'ummomin duniya sun yi kwararowa zuwa kasar Sin, jama'ar kasar Sin ba za ta manta da shi ba, kasar Sin ta nuna godiya ga dukkan duniya.

A cikin bayyanin, an bayyana cewa, a lokacin da kasar Sin take bukatar taimako ruwa a jallo, gamayyar kasa da kasa sun nuna babban juyayinsu ga bala'in girgizar kasa da ta fadawa a kasar Sin, kuma sun nuna alhini ga mutanen da suka rasu a sakamakon girgizar kasa, haka kuma sun nuna goyon baya ga kokarin da gwamnatin kasar Sin da jama'arsu suka yi wajen ceton mutane.

A cikin bayyanin, an bayyana cewa, bala'in daga indallahi zai iya aukuwa a dukkan duniya, duk da ko wace kasa ta yi barna, gwamnatin kasar Sin da jama'arsu za su ci gaba da bayar da iyakacin kokarinsu ga mutanen da suka bukaci taimako.(Bako)