Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-22 21:58:25    
An nemi da a ci gaba da yin matukar kokari domin yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane

cri
A ran 22 ga wata, an yi taron zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na J.K.S. don yin bincike da tsara shirin yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane. Mr, Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na J.K.S. ya shugabanci taron.

Taron ya bayyana cewa, har ila yau ana cikin hali mai tsanani wajen yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane, ya kamata a ci gaba da mai da wanan aiki bisa matsayi mafi muhimmanci kuma mafi gauggawa. Ya kamata a ci gaba da cigiya da ceton mutanen da ke shan wahalar bala'in, a yi kokarin aiki har ba za a rage mutum ko daya ba. Kuma ya kamata a ci gaba da warkar da mutaneda suka ji raunuka, da yin aikin rigakafin cututtuka da kyau don tabbatar da ganin ba a samu cututtuka masu yaduwa ba bayan da babban bala'in ya faru. Sa'an nan kuma ya kamata a mai da muhimmanci don sake tsugunar da jama'a masu fama da bala'in, ta yadda za a samu tabbaci sosai ga zaman rayuwar jama'a masu shan bala'in, musamman ma a mai da hankali sosai don sake tsugunar da marayu yara da tsofaffi da nakasassu. (Umaru)