Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-22 21:50:52    
Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin tana kokarin kyautata halin da kasuwanni ke ciki a shiyyar bala'i da farfado da tsarin jigilar kayayyaki

cri
A gun taron manema labaru da aka yi a ran 22 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Chen Deming, ministan kasuwanci na kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu ma'aikatar kasuwanci tana kokarin kyautata halin da kasuwanni ke ciki a shiyyoyin da bala'in ya shafa da farfado da tsarin jigilar kayayyaki. Ya zuwa ran 22 ga wata da safe, da akwai kasuwanni da yawansu ya wuce dubu 17 na larduna 3 wato Sichuan da Gansu da Shanxi wadanda suka sha illa sakamakon bala'in girgizar kasa sun riga sun sake bude kofofinsu.

Mr. Chen ya bayyana cewa, bayan da girgizar kasa mai tsanani ta faru a lardin Sichuan, ma'aikatar kasuwanci ta sanya iyakacin kokari don samar da kayayyakin agaji ciki har da ruwan sha da abinci da kayayyakin ceto da fitilu domin yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane. A halin yanzu kuma muhimmin aikin da ma'aikatar za ta yi shi ne aikawa da kayayyakin da ake bukata sosai zuwa kauyuka, kuma a mika su cikin hannayen mutane fararen hula wadanda suka fi shan wahalhalu sakamakon bala'in.

Mr. Chen ya kuma bayyana cewa, idan da sharadi, ya kamata a farfado da kasuwanni manya da kanana tun da wuri. (Umaru)