Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-22 20:19:03    
Mutane 51151 sun rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan

cri
Yau 22 ga wata, a gun taron manema labaru da aka shirya a nan birnin Beijing, Mr. Guo Weimin, kakakin ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya ce, bisa kididdigar da ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar ta yi, an ce, ya zuwa ranar 22 ga wata da karfe 10, mutane 51151 sun rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa mai karfin digiri 8 na ma'aunin Richter da aka samu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, yayin da mutane sama da dubu 280 ne suka ji rauni, kuma mutane fiye da dubu 29 suka bace.

Ya zuwa ranar 22 ga wata da karfe 2 da yamma kuma, kananan hukumomin kasar Sin sun bayar da kudade da yawansu ya kai kudin Sin RMB biliyan 13.975, don yaki da bala'in girgizar kasa. Ya zuwa ranar 22 ga wata da karfe 12, kasar Sin ta samu taimakon kudi daga gida da waje da yawansu ya wuce kudin Sin RMB biliyan 21.4. (Bilkisu)