Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-22 13:58:08    
Kafofin yada labaru na kasashen ketare sun yaba wa aikin ceton mutane da sojoji masu 'yantar da jama'a da 'yan sanda na kasar Sin suka yi

cri

Kwanakin nan, kafofin yada labaru na kasashen ketare sun ci gaba da dora muhimmanci sosai a kan matakan da sojojin kasar Sin suka dauka wajen yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane, haka kuma sun yaba wa matakan da sojojin kasar Sin suka dauka.

Manyan kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya da suka hada da kamfanin dillancin labaru na Associated Press da Routers da Agence France-press sun bayar da labaru cikin lokaci, don bayyana mana halin da bala'in girgizar kasa ta gundumar Wenchuan ke ciki da kuma yada labarun game da bayar da gudumawar agaji, kuma sun bayyana mana matakan da sojojin kasar Sin suka dauka wajen bayar da gudumawar agaji cikin lokaci. 'Dan jaridar Associated Press na kasar Amurka ya bayyana cewa, matakan da sojojin kasar Sin suka dauka na cikin lokaci ya bayyana mana shugabannin kasar Sin sun riga sun mayar da aikin bayar da gudummawar agaji ga bala'i gaban kome.

A wata sabuwa kuma, kwararru wajen ceton mutane na kasa da kasa su ma, su yaba wa matakan da sojojin kasar Sin suka dauka na bayar da gudummawar agaji. Ran 20 ga wata, a cikin aikin yin ta'aziyya ga mutanen da suka rasu a sakamakon girgizar kasa da aka yi a lardin Sichuan na kasar Sin a ofishin jakadancin Sin da ke kasar Jamus, ministan tsaron kasa na kasar Jamus Franz Josef Jung ya yaba wa matakan bayar da gudumawar agaji da sojojin kasar Sin suka dauka a yankunan da aka yi girgizar kasa a lardin Sichuan a kasar Sin.(Bako)