Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-22 13:29:23    
Firaministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya jaddada cewa dole ne a samar da goyon baya ta kimiyya wajen aikin yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane

cri

Ran 21 ga wata, a nan birnin Beijing, Wen Jiabao zaunannen mamben hukumar siyasa ta tsakiya ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma firaministan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, kuma babban direkta na hukumar ba da umurni kan aikin yaki da bala'in girgizar kasa da kuma ceton mutane ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya jaddada cewa dole ne a samar da goyon baya ta kimiyya wajen aikin yaki da bala'in girgizar kasa da kuma ceton mutane.

A gun taron da aka yi a wannan ranar kan kafa kwamitin kwararru wajen nazarin girgizar kasa da ta fadawa a gundumar Wen chuan a lardin Sichuan na kasar Sin, firaministan Sin Mr Wen Jiabao ya shugabanci taro, kuma ya bayyana cewa, kafa kwamitin kwararru wajen nazarin girgizar kasa ya samar da goyon baya ta kimiyya wajen yaki da bala'in girgizar kasa da aikin ceton mutane, haka kuma yana da muhimmanci sosai wajen tsugunar da mutane da kaddamar da aikin kawo albarka da sake farfado da wuraren da bala'in girgizar kasa ya shafa a kasar.

Bisa labarin da muka samu, an ce, kwamitin kwararru wajen nazarin girgizar kasa da ta fadawa a gundumar Wenchuan ta kasar Sin da aka kafa ba da dadewa ba, zai gudanar da aikin tantance bala'in girgizar kasa, haka kuma za su yi bincike da nazari a kan ilmin girgizar kasa, ta haka za su iya bayar da wasu shawarwari wajen aikin yaki da bala'in girgizar kasa da sake farfado da wuraren da bala'in girgizar kasa ya shafa. Kwamitin kwararru ya kunshe da manyan da kananan kwararrun da suka yi nazari a kan fannoni daban daban 30, kuma sun hada da mutane masu aikin a kwalejin nazari 13, da furofesa 17.(Bako)