Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-22 12:31:01    
Ana gudanar da aikin kwashe gawawwakin dabbobi a yankunan da aka yi girgizar kasa a lardin Sichuan na kasar Sin daga dukkan fannoini

cri
Ran 22 ga wata, bisa labarin da aka bayar, an ce, an riga an fara aikin kwashe gawawwakin dabbobi a yankunan da aka yi girgizar kasa a lardin Sichuan a kasar Sin daga dukkan fannoni, ya zuwa yanzu, an riga an kwashe dabbobi da yawansu ya kai miliyan 10.

Yanzu, likitocin da yawansu ya kai dubu 10 wajen rigakafin cututtuka suna aikin sa idon a garuruwan da ke yankunan da aka yi girgizar kasa, kuma sun kwashe gawawwakin dabbobi a gandun kiwon dabbobi a yankunan da aka yi girgizar kasa. Ministan noma da ke jagorancin aikin yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane na kasar Mr. Sun Zhengcai ya bayyana cewa, yanzu aikin da ke gaban kome shi ne yin rigakafi ga cututukka, dole ne hukumomi daban daban wajen aikin noma na kasar su kara taimaka wa manoma da ke yankunan da aka yi girgizar kasa wajen girbe hatsi da kuma yin shuke-shuke, da yin kokari ba tare da kasala ba wajen taimaka wa yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su wajen farfado da aikin kawo albarka.(Bako)