Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 22:10:22    
zaman makoki a kasar Sin ya bayyana manufar mayar da jama'a a gaban kome, in ji kafofin yada labarai na ketare

cri
Kwanan nan, wasu kafofin yada labarai na kasashen ketare sun bayar da sharhohi, inda suke ganin cewa, tsai da kudurin yin zaman makoki a duk fadin kasar Sin tun daga ran 19 har zuwa 21 da gwamnatin Sin ta yi, ya dace da al'adar gargajiya ta kasar Sin, kuma ya bayyana manufar mayar da jama'a a gaban kome.

Jaridar Lianhe Zaobao ta kasar Singapore ta ce, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin zaman dokoki a duk fadin kasar cikin kwanaki uku, wannan ba ma kawai ya dace da al'adar gargajiya ta kasar Sin ba, haka kuma ya nuna mana wayin kai na kasar Sin. Kudurin ya nuna girmamawa ga rayukan jama'a, kuma ya mayar da jama'a a gaban kome. A cikin kwanakin nan uku, an dakatar da mika wutar wasannin Olympics, wannan ya nuna cewa, moriyar jama'a ta fi kome, kuma ana aiwatar da manufar mayar da jama'a a gaban kome kamar yadda ya kamata.

Bayan haka, a ran 20 ga wata, jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya ta bayar da sharhi a shafinsa na internet cewa, Sin ta yi zaman makoki na musamman na kwanaki uku domin jama'arta da suka rasa rayukansu, ban da wannan, gwamnatin kasar ta kuma dakatar da mika wutar wasannin Olympics a cikin kwanakin nan uku, wannan ya nuna mana sabon tunanin kasar Sin na shiga cikin gamayyar kasa da kasa.(Lubabatu)