Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 21:28:24    
Shugabanni daga kasashe da kungiyoyi daban daban na duniya sun nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan

cri
'Yan kwanakin da suka wuce, shugabanni daga kasashe da bangarori daban daban na kasashen duniya sun je ofisoshin jakadanci na kasar Sin da ke kasashen waje, da ofisoshin wakilai na kasar Sin da ke kungiyoyin kasashen duniya, don nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon babbar girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan. A waje daya kuma, kasashen duniya suna cigaba da bayar da taimako ga kasar Sin, don yaki da bala'in.

Firayin ministan kasar Japan Mr. Fukuda Yasuo, da shugaban kasar Colombia Mr. Alvaro, da shugaban kasar Pakistan Mr. Pervez Musharraf, da shugaban kasar Faransa Mr. Nicolas Sarkozy, da shugaban kasar Amurka George W. Bush, da kuma shugaban kasar Korea ta kudu Lee Myung-Bak, da dai sauransu, sun kansu sun je ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke kasashen, don nuna juyayi.

A waje daya kum, jami'ai daga wasu kunyiyoyin kasashen duniya sun je hukumomin kasar Sin da ke kasashen waje, don yin jimami, ciki har da babban sakataren M.D.D. Ban Ki-Moon, da babbar daraktar WHO madam Chan Fung Fu Chun, da kuma shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya Jacques Rogge.

Bayan haka kuma, ya zuwa yanzu, kasashe da kungiyoyin kasashen duniya da yawa, sun bayar da taimako ga yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa a fannonin samar da kayayyaki, da aikin likitanci, da kuma taimakon kudi. (Bilkisu)