Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 21:21:21    
Kasa Sin tana kashe kwayoyin cuta da kuma yin rigakafi a wuraren da ke fama da bala'i daga dukkan fannoni

cri

Ya zuwa yanzu a lardin Sichuan inda ake fama da bala'in girgizar kasa, mutane masu aikin ceto suna ci gaba da kokarin neman wadanda ke da sauran numfashi. A sa'i daya kuma, an riga an fara yin ayyukan kashe kwayoyi cuta da yin rigakafi daga dukkan fannoni. Bisa kididdigar da aka yi, yanzu duuban mutane masu fasaha suna yin ayyukan kashe kwayoyin cuta, suna kokarin yin ayyukan kashe kwayoyin cuta da kuma daidaita matsalolin gawawwaki a birane ko gundumomin. Saboda kokarin da suka yi, ya zuwa yanzu, ba a sami labarin manyan yaduwar cuta da hadarin lafiya ba.Yanzu ga labarin da wakilnmu Mr. Gong Wangpeng ya ruwaito.

Mutane da yawa sun mutu ko jikkata a sakamakon girgizar kasa da ta faru a lardin Sichuan a ran 12 ga wata. Saboda akwai gawawwaki da yawa, kuma akwai shara na zaman yau da kullum, tare kuma kasancewar hadarin faruwar cututtuka masu yaduwa. Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin, ta riga ta aika da dubban mutane masu fasaha zuwa wurin bala'in domin yin ayyukan kashe kwayoyin cuta. Ya zuwa ran 19 ga wata, yawan wuraren da aka kashe kwayoyin cuta ya kai muraba'in mita kimanin miliyan 100, yawan gawawwakin da aka binne ya kai fiye da 8400. Musamman ma a wasu wuraren da suke fuskanci matsananciyar wahala, an yi ayyukan kashe kwayoyin cuta daga dukkan fannoni.

Tun daga ran 13 ga wata, Mr. Feng Yan ma'aikacin kashe kwayoyin cuta ya shiga gundumar Beichuan, yana yin aikin tsawon awoyi fiye da 12 a ko wace rana. Ya ce, "Ko wace rana muna aikin tun daga karfe 7 na safe zuwa karfe 6 na yamma.muna da cikakken kayayyakin kashe kwayoyin cuta, kuma muna kare kanmu sosai."

Bisa labarin da muka samu, an ce yanzu yawan ma'aikatan kashe kwayoyin cuta ya kai fiye da 100 a gundumar Beichuan. Mr. Hu Yong shugaban cibiyar shawo kan cututtuka ta birnin Mianyang ya nuna cewa, an riga an sami kyakkyawan sakamako wajen kashe kwayoyin cuta a birnin Mianyang. Ya ce, "Ba mu jin tsoron gajiya, mun dauka ingantattun matakai domin kashe kwayoyin cuta ta hanyar kimiya, ya zuwa yanzu, an sami kyakkyawan sakamako."

Bisa labarin da muka samu, an ce, ana aiwatar da ayyukan kashe kwayoyin cuta a gundumomin Wenchuan da Qingchuan da sauran wuraren da ke fama da bala'in daga dukkan fannoni, wannan ya sami kyakkyawan sakamako wajen hana faruwar cututtuka. Ban da haka kuma, hukumomin da abin ya shafa sun kara sa ido kan wurin da ake samar da ruwan sha, da kamfannonin dafa abinci, da hukumomin kiwon lafiya, da kuma wuraren da ake kwatar da mazaunan da suke shan wahala, kuma ana ba da ilmin yin rigakafi ga mutanen da ke fama da bala'i da kuma wadanda ke shan wahala..

Mr. Hu Yong ya fayyace cewa, bisa shirin yin rigakafi da aka yi, bayan an kammala ayyukan ceto, za su cigaba da yin ayyuka a wuraren da ke fama da bala'i. Ya ce,  Bayan da dukkan mutane masu ayyukan ceto su janye, za a cigaba da kashe kwayoyin cuta, da kuma sa ido kan ingancin ruwan sha, da binne gawawwaki, ya kamata mu mutane masu aikin yin rikakafi za mu janye a karshe."

A ran 20 ga wata, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta sanar da cewa, ya zuwa yanzu, ba a sami yaduwar cututuka a wuraren da ke fama da bala'in ba. Amma cibiyar yin rigakafin cututuka ta kasar Sin ta riga ta kafa tsarin tarar da labarin yaduwar cututuka ta wayar salula. A sa'I daya kuma, ma'aikatar kiwon lafiya ta yanke wata shawara, wato tun daga ran 20 ga wata, za a kara aika da mutane fiye da 2500 domin kara yin ayyukan kashe kwayoyin cuta da yin rigakafi a wuraren da ke fama da bala'in.