Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 20:53:39    
Mutane 41353 sun rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan

cri

Bisa rahoton da ma'aikatar harkokin jama'a ta kasar Sin ta bayar an ce, ya zuwa ranar 21 ga wata da karfe 12, mutane 41353 sun rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa mai karfin digiri 8 na ma'aunin Richter da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, yayin da mutane 274683 suka ji rauni, kuma mutane 32666 suka bace.

A ranar 21 ga wata, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar da sanarwa cewa, ya zuwa ranar 21 ga wata da karfe 12, jimlar taimakon kudin da kasar ta samu daga gida da waje ta kai kudin Sin RMB biliyan 16.009.

Kazalika kuma, bisa rahoton da ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta bayar an ce, ya zuwa ranar 21 ga wata da karfe 12, mutanen da ake yi masu jiyya a asibitoci sun kai 59394, wadanda 30289 suka fita daga asibitoci.

Bugu da kari kuma, ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta bayar da rahoto cewa, ya zuwa ranar 21 ga wata da karfe 2 na yamma, kananan hukumomin kasar sun zuba kudaden da yawansu ya kai kudin Sin RMB biliyan 12.867, don yaki da bala'in girgizar kasa. (Bilkisu)