Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 16:48:06    
Shugabannin kasashen waje da jami'an kungiyoyin duniya da mutane masu sana'o'i daban daban sun je ofishin jakadancin Sin da ke kasashen waje don nuna jejeto ga mutane da suka mutu a sakamakon bala'in girgizar kasa

cri
Kwanakin uku watau daga ran 19 zuwa ran 21 ga watan Mayu sun zama ranakun zaman makoki a kasar Sin, ofishin jakadancin Sin da ke kasashen waje sun saukar da tutar kasa zuwa rabin sanda don yin ta'aziyya ga mutanen da suka rasu a sakamakon girgizar kasar, haka kuma ofishin jakadancin Sin da ke kasashen waje sun kafa wuraren rubuta kalmomin juyayi ga mutanen da suka mutu. Shugabannin kasashen waje da dama da mutane masu sana'o'i daban daban da 'yan diplomasiyya na kasashen waje sun je ofishin jakadancin Sin da ke kasashen waje don nuna babban juyayinsu ga mutanen da suka rasu a sakamakon girgizar kasa da aka yi a gundumar Wenchuan a lardin Sichuan ta kasar Sin.

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza da takwaransa na kasar Mauritius da na kasar Faransa da na kasar Croatia da na kasar Peru da kasar Amurka da kasar Koriya ta kudu sun mika kwandon furanni ga mutanen da suka rasu. Shugaban kasar Serbia Tadiqi ya tura wakilai watau shugaba mai ba da shawara Yin Jiqi don ya je ofishin jakadancin Sin da ke kasar Serbia yin ta'aziyya. Ran 21 ga wata, firaministan kasar Japan Fukuda Yasuo ya nuna ta'aziyya ga mutanen da suka rasu a girgizar kasa a ofshin jakadancin Sin da ke kasar Japan, ya bayyana cewa yana fatan aikin yaki da girgizar kasa da kuma ceton mutane zai kara samun sakamako mai kyau, don sake gina wuraren da bala'in ya shafa da kuma farfado da zaman rayuwar mutane a yankunan da bala'in ya ritsa da su tun da wurwuri.

A sa'i daya kuma, wasu jami'an kungiyoyin duniya su ma sun je ofishin jakadancin waje da ke kasar Sin don yin ta'aziyya. Sakataren janar na kasar Sin da ke M.D.D Ban Ki-Moon ya nuna ta'aziyya ga mutanen da suka rasu a sakamakon da girgizar kasa da aka yi a wenChuan a kasar Sin a ofishin wakilan Sin da ke M.D.D, kuma ya bayyana cewa, yayin da muka fuskanci babban kalubale, gamayyar kasa da kasa da mutanen kasar Sin suna tsaya a bai daya tare. Ran 20 ga wata, jami'in hukumar kiwon lafiya ta duniya Chan Fung Fu Chun ya yi ta'aziyya ga mutanen da suka rasu a sakamakon girgizar kasa da aka yi a Wenchuan a kasar Sin, kuma ya yaba wa aikin ceton mutane da aka yi mai amfani. Ran 20 ga wata, kwamitin gasar wasannin Olympic ta duniya Jacques Rogge ya bayyana cewa, ya nuna babban juyayi ga mutanen da suka rasu a yankunan bala'in girgizar kasar Sin, kuma ya jaddada cewa gasar wasannin motsa jiki ta Olympic tana bai daya tare da mutanen da suka rasu a sakamakon bala'in girgizar kasar.(Bako)