Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 16:02:27    
Kasashen Jordan da Italy da Ukraine da Japan da Jamus sun samar da tallafin kaya da na aikin jiyya ga kasar Sin

cri
A cikin 'yan kwanakin nan, bi da bi ne kasashen Jordan, da Italy, da Ukraine, da Japan, da Jamus suka samar da kayan agaji da tallafin aikin jiyya ga yankunan da mummunan bala'in girgizar kasa ya shafa a Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin.

Da sanyin safiyar yau 21 ga wata, kayayyakin agajin da daular Hashemite ta Jordan ta bayarwa yankunan da bala'in girgizar kasa ya shafa a lardin Sichuan suka isa filin jirgin sama na Shuangliu a birnin Chengdu.

Yau 21 ga wata, wata majiya daga ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, kasar Italy ta riga ta samarwa bangaren Sin tallafin kudin EURO miliyan guda da kayayyakin agajin da darajarsu ta kai kudin EURO miliyan 1.5. Kazalika kuma, za ta samarwa kasar Sin wani kyakkyawan asibitin tafi-da-gidanka, tare kuma da mutane masu aikin jiyya guda 16.

A waje daya kuma, da misalin karfe 1 da minti 10 na maraicen yau ne, kayayyakin agaji na kashin farko da Ukraine ta samarwa yankunan da bala'in girgizar kasa ya shafa a lardin Sichuan suka isa birnin Chengdu. Nauyin kayayyakin agajin ya kai ton 40, ciki har da tantuna, da kayayyakin aikin jiyya da dai sauransu.

Kungiyar masu aikin jinya ta kasar Japan ta isa birnin Chengdu cikin jirgin saman musamman jiya da dare. A cikin jirgin saman, akwai kayayyakin agaji na aikin jinya da nauyinsu ya kai ton 5 wadanda ake nemansu ruwa a jallo a yankunan da bala'in girgizar kasar ya rutsa da su.

Bugu da kari kuma, kungiyar bada agaji ta farko ta kasa da kasa wadda ke kunshe da kwararrun Jamus sama da 10 ta riga ta isa lardin Sichuan a shekaranjiya da dare, inda Sin da Jamus za su kafa wani asibiti a fili cikin hadin-gwiwa.(Murtala)