Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 12:16:24    
Wen Jiabao ya bukaci da a gudanar da ayyukan tsugunar da fararen hula masu fama da girgizar kasa yadda ya kamata

cri

A ran 20 ga wata, Wen Jiabao, zaunannen memban hukumar siyasa ta tsakiya ta JKS kuma firayim ministan kasar Sin kuma babban mai ba da umurni na babban ofishin ba da umurni kan fama da girgizar kasa da gudanar da ayyukan ceto na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya jaddada cewa, ya kamata a gudanar da ayyukan tsugunar da fararen hula masu fama da bala'in kamar yadda ya kamata da kuma rigakafin bala'i na mataki na biyu.

A ran nan, Wen Jiabao ya shugabanci taro na 11 na babban ofishin domin nazarin ayyukan tsugunar da fararen hula masu fama da bala'in da kuma rigakafin bala'i na mataki na biyu. Taron ya tsai da kudurin cewa, a 'yan kwanaki masu zuwa, za a bukaci sake tura tantuna dubu 40 zuwa yankuna masu fama da bala'in, da kuma daukar dakunan kwana 6000 na rukunin farko zuwa yankunan a cikin kwanaki biyu masu zuwa, da kuma dudduba da binciken matarin ruwa da suka fi saukin samun hadari bi da bi domin kau da hadari da kara ingancinsu nan da nan. Haka kuma za a kara sa ido kan tafkin Yansai da ya fi saukin samun hadari, da tattara kwararru wajen kimantawa daga dukkan fannoni domin tsara shirin kawar da hadari da kuma gudanar da aikin kau da hadarin.(Kande Gao)