Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 12:13:57    
Za a tabbatar da zaman rayuwar mutanen da suak rasa iyali na yankuna masu fama da girgizar kasa

cri

Ma'aikatar kudi ta gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin samar da kudin taimako Yuan 600 ga ko wane maraya da ko wane tsoho da kuma ko wane mutum nakasasshe da ya rasa dukkan 'yan iyali a cikin wannan girigrizar kasa da ta auku a lardin Sichuan na kasar Sin a ko wane wata domin tabbatar da zaman rayuwarsu.

Jiang Li, mataimakin ministan kula da harkokin jama'a na kasar Sin ya yi bayani a gun taron manema labarai da aka shirya a ran 20 ga wata, cewa yanzu an riga an samu mutane 124 da ba su da 'yan iyali, ciki har da marayu fiye da 70 da kuma tsoffi  da nakasassu fiye da 40. A nan gaba lardin Sichuan zai sake gina wasu gine-ginen jin dadin jama'a domin ciyar da wadannan mutane.(Kande Gao)