Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 21:42:40    
(Sake Sabunta)Shugabanni na kasashe da yawa sun je ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke kasashen waje domin nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa

cri

A 'yan kwanakin baya, bi da bi ne, shugabannin kasashe daban daban ciki har da Kodivwa, da Korea ta arewa, da Peru, da Ecuatorial Guinea, da Chile, da Lebanon da dai sauransu suka je ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke kasashen waje domin nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa.

A ran 19 ga wata da safe, shugaban kasar Peru Mr Alan Garcia ya zo ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasarsa. Ya yaba wa aikin ceto da gwamnatin kasar Sin take gudanarwa cikin sauri, ya kuma yi imani cewa, kasar Sin za ta iya cin nasarar yaki da bala'in girgizar kasa, haka kuma za ta ci nasarar shirya gasar wasannin Olympics.

A ran 19 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Kodivwa Mr. Youssouf Bakayoko ya je ofishin jakadancin kasar Sin da ke Kodivwa, domin nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu sakamkon babbar girgizar kasa da ta faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin.

A ran 20 ga wata da safe, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Vietnam, kuma mataimakin sakataren hukumar Jam'iyya ta sojoji ta kwamitin tsakiya, kuma ministan tsaron kasar Vietnam ya je ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasarsa, domin nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasar Sin.

Ban da wannan kuma, shugabannin kasar Korea ta arewa, da na Mongolia, da mataimakin shugaba na farko na kasar Peru, da kuma firayin minista da kuma ministoci 10 na kasar, da firayin ministan kasar Ecuatorial Guinea, da shugabannin majalisun dattawa da wakilai, da ministan harkokin waje na kasar Lebanon, da shugaban majalisar wakilai ta kasar Japan su ma sun mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu sakamkon babbar girgizar kasa.(Danladi)