Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 20:25:33    
An fara kai wadanda suka ji raunuka sakamakon girgizar kasa a lardin Sichuan zuwa birane da larduna daban daban na kasar Sin

cri

A jiya 19 ga wata da dare, bisa rakiyar likitoci 60 ne, wani jirgin kasa da ke dauke da mutane 208 da suka ji raunuka sakamakon girgizar kasa mai tsanani da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan da ke kudu masu yammacin kasar Sin, ya isa tashar jiragen kasa da ke birnin Chongqing. Wannan ne karo na farko da aka kai masu raunuka sanadiyyar girgizar kasar zuwa asibitocin biranen da ke waje da lardin Sichuan.

Yawancin mutanen da ke cikin jirgin sun zo ne daga garin Mianyang. Yankin Mianyang na daya daga cikin yankunan da girgizar kasa ta fi yi wa barna, sabo da haka, asibitoci daban daban na cike da mutanen da suka ji raunuka masu tsanani. A yayin da ake gudanar da aikin agaji zuwa garuruwa daban daban, karin masu raunuka a sanadiyyar girgizar kasar za su isa birnin Mianyang. Sabo da haka, tun daga ran 18 ga wata, birnin Mianyang ya fara kai masu raunuka 2100 daga asibitoci 9 da ke birnin da kuma asibitocin da ke garin Jiangyou da garin Anxian zuwa birnin Chongqing.

Domin kai su birnin Chongqing kamar yadda ya kamata, sassan sufurin jiragen kasa na wurin sun kashe kwayoyin cuta a jirgin kasar da zai yi jigilar masu raunuka, bayan haka, an kuma sanya na'urorin agaji da ya kamata a cikin jirgin. Ma'aikatan jirgin ma an yi musu horaswa na musamman daga kungiyar Red Cross.

Kafin jirgin kasa ya isa tashar jiragen kasa da ke birnin Chongqing, daruruwan likitoci da motocin agaji 208 sun riga sun isa suna jira. Malama Li Xuechun, wata likita da ke jira a wurin, ta ce,"akwai likitoci da yawa a cikin jirgin kasa, kuma suna lura da su yadda ya kamata. Yanzu da farko, za mu bincika ko sun kamu da cututtuka masu yaduwa, idan babu matsala, to, za mu sa su a motocinmu. Daga bisani kuma, za mu kai su asibitoci. Asibitoci sun riga sun share fage."


1 2