Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 19:45:10    
Jakadan kasar Algeria da ke nan kasar Sin, ya isar da taimakon kudi ga ma'aikatar harkokin waje ta Sin

cri
Jiya 19 ga wata a nan birnin Beijing, bisa gayyatar da aka yi masa, Mr. Song Aiguo, shugaban sashen kula da harkokin Asiya da Afrika na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, ya gana da Mr. Djamel Eddine Grine, jakadan kasar Algeria da ke kasar Sin, inda ya karbi caki na dalar Amurka miliyan daya da gwamnatin kasar Algeria ta bayar gudumawa don bala'in girgizar kasa da aka samu a Wenchuan na lardin Sichuan na kasar Sin.

Mr. Grine ya bayyana cewa, shugaba Abdelaziz Bouteflika, da gwamnatin kasar Algeria, da kuma jama'ar kasar sun nuna juyayi ga gwamnati da jama'ar kasar Sin, da kuma jajantawa iyalan jama'ar da suka mutu sakamakon girgizar kasa.

Mr. Song Aiguo ya bayyana cewa, a muhimmin lokaci wajen yaki da bala'in da kasar Sin ke yi, kasar Algeria ta bayar da taimako ga kasar Sin, wannan ya nuna dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu. (Bilkisu)