Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 15:59:03    
Hukumomin harkokin waje da ke kasashen waje na kasar Sin da Sinawa mazaunan waje sun yi jimami ga mutanen da suka mutu a bala'i

cri

Ran 19 ga wata, bi da bi ne ofisoshin jakadun kasar Sin da ke kasashen waje, da ofisoshin wakilan kasar Sin da ke kungiyoyin kasa da kasa, da hukumomin jarin kasar Sin da ke kasashen waje da Sinawa mazaunan kasashen waje sun yi jimami ga mutnanen da suka mutu a sakamkon bala'in girgizar kasa da ya faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan.

Tun daga ran 19 ga wata da sassafe a nan birnin Beijing, bi da bi ne ofisoshin jakadun kasar Sin da ke kasashen waje, da ofisoshin wakilan kasar Sin da ke kungiyoyin kasa da kasa, da hukumomin jarin kasar Sin da ke kasashen waje da ke kasashe dabam daban sun saukar da tutocin kasa zuwa rabin sanda domin nunawa jimami ga mutanen da suka mutu. Ban da haka kuma, sun kafa kundin rubuta kalmomin ta'aziyya.

A wannan rana da karfe 2 da minti 28 bisa agogon Beijing, sun yi tsit na tsawon mintoci 3 tare da dukkan jama'ar kasar Sin domin nunawa ta'aziyya ga mutanen da suka mutu.