Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 15:43:27    
Kafofin watsa labaru na kasa da kasa suna lura da ayyukan nuna jimami da kasar Sin take yi

cri

Ran 19 ga wata rana ce ta farko da ke cikin ranakun yin makoni na duk kasar Sin domin nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa da kasar Sin, a wannan rana, bi da bi ne kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun yi rahoto kan ayyukan ta'aziyya da kasar Sin ta yi a wurare dabam daban, musamman ma kan aikin yin tsit domin nuna jimami a wannan rana da yamma.

Kamfanin dilancin watsa labaru na AP ya ce, a daidai lokacin da girgizar kasa ta faru yau da kwanaki 7 da suka wuce a gundumar Wenzhuan da ke lardin Sishuan na kasar Sin, jama'ar duk kasar sun yi tsit cikin mintoci 3 don yin ta'aziyya ga mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar, kuma motoci da jiragen kasa da na ruwa da ke wurare daban-daban sun yi ta kararawa.

Ban da haka kuma, BBC, da CNN da manyan telebijin na kasar India sun ba da wannan labari.

Kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun samu manyan tashoshin Internet na kasar Sin da yawancin jaridun kasar Sin sun yi amfani launin baki da fari, kuma sun rubutu "ranakun yin ta'aziyya na duk kasar Sin"a fili mai muhimmanci.