Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 15:35:45    
Wurin Jiu Zhai gou shahararren wuri mai ni'ima na kasar Sin

cri

A cikin wannan shiri, za mu gabatar muku abubuwan da wakilin rediyonmu ya rubuto mana, bayan da ya kai ziyara a shahararren wuri mai suna Jiu Zhai geu. A shekara ta l992, kungiyar Unesco ta majalisar dinkin duniya ta mai da wurin halitta mai suna Jiu Zhai geu da ya zama kayan halitta na gargajiyya na tarihi na matsayin duniya.

Wurin Jiu Zhai geu yana cikin shiyyar kabilar Jiang mai ikon tafiyar da harkokin kanta da Jihar Tibet ta lardin Schuan dake kudu maso yammancin kasar Sin, tsawon wurin nan yana da kilomita fiye da 40, a cikin wannan wuri, akawai kwari da tafki da mafadar ruwa da tuddai masu kankara da taushi da gandun daji, kai halitta ta wannan wuri mai kyan gani sosai da sosai, har yana shahara a duk kasar Sin da na kasashen waje. A wannan wuri, akwai manya ko kananan tafkuna masu launi iri iri dake kan manyan tuddai, mutane na kabilar Tibet suna kiran irin wadannan tafkuna "Hai zh", kuma wadannan tafkuna suna hade da mafadar ruwa, kuma kewayensu akwai gandun daji da yawa masu tsanwa shar, kai wannan wuri mai ban mamaki sosai, a tsakanin wadannan gandun daji da tafkuna akwai kauyuka guda 9, saboda haka ne ana kiran wurin Jiu Zhai geu.

Dalilin da ya sa wurin Jiu Zhai geu yana da kyan gani haka, saboda ruwa da yawa a nan, Ruwan tafkuna yana da tsabta sosai, kaman madubi, abin mamaki shi ne launinsu ya sha banban sosai. Kana kuma wani tafkin dake tsakiyar wuri mai susna "Faranni 5", wato launinsa yana iya canjawa, amma yawancin lokaci, launinsa mai shudi sosai kaman ulu ulu mai daraja. Shin me ya sa launin wannan tafki ya iya canjawa? Wani mallami mai suna Fan shiao shi ne mai bincike labarin kasa na kungiyar binciken labarin kasa ta lardin Schuan kullum yake bincike wannan dalili, ya ce, domin wannan tafki yana da tsabta sosai kaman madubi, saboda haka ne an iya duba shi har zuwa zurfin tafki, koda yake wannan ruwa ba ya da launi, amma in akwai hasken rana sai launin wannan ruwan tafki ya iya canjawa iri iri. Ban da haka kuma, Mr.Fang ya ce, akwai wani dalilin daban da aka yi haka, domin wurin Jiu Zhai geo yana cikin layin taswirar duniya da kyau, a cikin ruwan tafki akwai wani irin abubuwa, wadannan abubuwa sun kara karfin launin ruwan tafki. A wurin Jiu Zhai geo ban da tafkuna da yawa, an kuma kasance da gandun daji masu fadi kadada fiye da dubu 30, an kuma kasance da ire iren shuke shuke masu daraja har sun kai fiye da 2500.

Sabo da wurin Jiu Zhai geo shi ne wurin halitta mai ni'ima sosai na kasar Sin, sai kullm yana jawo masu yawon shakatawa da yawa na gida da na kasashen duniya. A banbamcin yanayi, sai launinsa ya yi ta canjawa, Misali a yanayin bazara, a ko ina, ga shuke shuke masu tsanwa shar da suka fito daga kasa suna girma da sauri, dukkan abubuwan halitta masu rai masu kuruciya, a wannan lokaci ga ruwan da suka malala sannu sannu, koda yake akwai iska amma ba karfi, mutane suna jin dadi sosai, ga mafadar ruwa suna da yawa, kai kaman ruwan duniya, A wannan yanayi, masu yawon shakatawa sun fi yawa sosai. A yanayin hunturu, koda yake akwai sanyi, amma kuma akwai kankara mai taushi da surufe tafkuna, kaman wani babban mashimda dake rufe tafkuna, A yanayin kaka, ga launin yawancin shuke shuke sun yi canjawa, har ya zama mai rawaye.

A wannan wuri, akwai mutanen kabilar Tibet sukan kafa tanti, kuma suna son maraba da bakin da suka kai ziyara a tantinsu don sha nono, Bugu da kari kuma mutane na kabilar Tibet suna son yin wake wake da raye raye, cike da fara'a ne za ka iya more zaman jindi a duk wurin da za ka sa kafa.

Saboda wurin Jiu zhai geo ba wani wuri mai ni'ima kawai ba, hatta ma yana da daraja sosai wajen bincike shuke shuke masu daraja a duk duniya, Wani mallami mai bincike kayayyakin tarihi na gargajiya na duniya na kasar Sin ya gaya wa wakilin rediyonmu cewa, abubuwan halitta na wurin Jiu zhai geo suna daraja sosai, a nan ana iya bincike zurfin ilmin shuke shuken tarihin da suke kasancewa har yanzu. Musamman a wurin nan akwai gandun daji da yawa masu tsawon tarihi da suka kasancewa tun fil azal, Ya kamata za mu ci gaba da bincike dalilin kasancewar haka. To, jama'a masu sauraro, mun dai gabatar muku wani bayanin da wakilin rediyon kasar Sin ya rubuto mana, bayan da ya kai ziyara a wurin Jiu zhai geo mai ni'ima sosai har da ya shahara a gida da na kasashen waje.