Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 15:13:02    
An fara watsa shirye-shiryen ba da taimako kan halin dan Adam

cri

Ran 18 ga wata, a karo na farko ne Rediyon kasar Sin da Rediyon jama'ar kasar Sin ta tsakiya sun fara watsa shirye-shirye mai suna "Aikin ba da taimako kan halin dan Adam bayan bala'i", a cikin wannan shirye-shirye, masu ilmin halin dan Adam na gida da na waje za su ba da taimako na musamman ga mutanen da ke fama da bala'i.

Cibiyar nazarin halin dan Adam ta hukumar kimiyya ta kasar Sin, da kungiyar nazarin halin dan Adam ta kasar Sin su ne suka fara wannan shirin "Aikin ba da taimako kan halin dan Adam bayan bala'i" A cikin wannan shirye-shirye, masu ilmin halin dan Adam da kungiyar nazarin halin dan Adam ta yi ma'amala tare da mutanen da ke fama da bala'in kai tsaye. Ban da haka kuma, shirye-shiryen da rediyon kasar Sin zai watsa suna kunshe da karin bayanin da aka yi kan ilmin ba da agaji ga halin dan Adam.

Bisa bayyanin da aka yi, an ce, za a yi wannan shirye-shirye a dogon lokaci mai zuwa. Kuma wannan shirye-shirye ya nuna burin mutane masu aikin watsa labaru, da masu ilmin halin dan Adam wajen ba da gudumawa ga yaki da bala'in girgizar kasa da ba da ayyukan ceto.