Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 14:23:19    
Panda 3 sun bace, hukumar gandun daji ta kasar Sin za ta kara sa ido kan panda a daji

cri

Yanzu, akwai panda 3 na yankin kiyaye muhallin halitta mai suna "Wo Long" na lardin Sichuan da suka bace a lokacin bala'in girgizar kasa, sauran panda 60 suna nan lafiya lau.

Bayan bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, hukumar gandun daji ta kasar Sin ta tura rukuni zuwa lardin Sichuan don jagorancin aikin ceto a fannin daji da kula da aikin ceton panda, musamman ma dudduba ayyuka da na'urori da gine-gine na yankin kiyaye muhallin halitta mai suna "Wolong".

Bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan ya kawo cikas ga yankunan da panda suke zama a lardin Sichuan da lardin Shanxi. Hukumar gandun daji ta kasar Sin ta furta cewa, za ta kara sa ido kan panda da suke zama a daji, za ta yi musu jiyya idan an gano panda wadanda suka ji rauni.(Lami)