Bisa labarin da muka samu daga ma'aikatar kudi ta kasar Sin, an ce, ya zuwa karfe 3 na yamma na ranar 19 ga wata, hukumomin kudi daban daban na kasar Sin sun kebi kudin da yawansu ya kai kudin Sin Yuan biliyan 7 da miliyan 794 wajen yaki da girgizar kasa.
Bisa labarin da muka samu daga ma'aikatar harkokin jama'ar kasar Sin, an ce, ya zuwa karfe 1 na yamma na ranar 19 ga wata, dukkan jama'ar kasar Sin sun bayar da kyautar kudi da kayayyaki da yawan darajarsu ya zarce kudin Sin Yuan biliyan 10.8.(Danladi)
|