Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-19 21:33:26    
Hukumomin kasar Sin da ke wakilci a kasashen waje sun nuna alhini da ta'aziyya sosai ga wadanda suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan

cri
Yau da yamma, da misalin karfe 2 da minti 28, agogon birnin Beijing, ma'aikatan ofisoshin jakadancin kasar Sin a kasashen waje da na ofisoshin wakilan kasar Sin a kungiyoyin duniya da na hukumomi masu jarin kasar Sin da kuma sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin sun yi tsit tare da jama'ar kasar Sin cikin tsawon mintoci 3, don nuna alhini ga wadanda suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasa mai tsanani da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin.

Tun daga ran 19 ga wata da safe, agogon birnin Beijing, bi da bi ne aka saukar da tutar kasar Sin zuwa rabin sanda a ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke kasashen waje da ofisoshin wakilan kasar Sin da ke kungiyoyin duniya da kuma inda hukumomi masu jarin kasar Sin da sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin suke a kasashen waje, don nuna alhini ga wadanda suka riga mu gidan gaskiya sakamakon girgizar.(Lubabatu)