Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-19 21:31:46    
Mr. Wen Jiabao ya shugabanci taro na 10 na babbar hedkwatar ba da jagoranci wajen yaki da girgizar kasa

cri

A ran 19 ga wata da yamma, zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, kuma firayin ministan kasar Sin, kuma babban jagora na babbar hedkwatar ba da jagoranci wajen yaki da girgizar kasa da gudanar da aikin ceto ya shugabanci taro na 10 na hedkwatar, domin saurarar rahotanni da aka gabatar dangane da neman wadanda ke da sauran numfashi, da warkar da wadanda suka ji rauni, da sarrafa matsalolin da ke tasowa sakamakon rasuwar mutane, da kuma yin rigakafin cututtuka a yankunan girgizar kasar.

Abubuwan da aka tattauna a gun taron sun hada da kara yawan yankunan da ake neman wadanda ke da sauran numfashi, sojoji za su yi kokari sosai, domin tabbatar da shiga cikin dukkan kauyuka cikin awoyi 24, da kuma gudanar da ayyukan rigakafin cututtuka yadda ya kamata, jigilar kayayyakin likitanci da magunguna zuwa dukkan yankunan girgizar kasa, da sarrafa matsalolin da ke tasowa sakamakon rasuwar mutane yadda ya kamata da dai sauransu.(Danladi)