Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-19 21:26:33    
Kasar Sin ta tsai da ranakun zaman makoki na kasar domin nuna alhini ga mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa

cri

Jama'a masu karanta shafuffukanmu na internet, yanzu ga shirinmu na "Mu leka kasar Sin." Umaru ne ke jan akalar filin.

A ran 19 ga wata da yamma misalin karfe 2 da minti 28, wato daidai lokacin da girgizar kasa ta faru yau da kwanaki 7 da suka wuce a gundumar Wenzhuan da ke lardin Sishuan na kasar Sin, jama'ar duk kasar sun yi tsit cikin mintoci 3 don yin ta'aziyya ga mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar, kuma motoci da jiragen kasa da na ruwa da ke wurare daban-daban sun yi kararawa. Shugabannin Sin ciki har da Hu Jintao da Wu bangguo da Wen Jiabao sun tsaya cik don yin ta'aziyya ga mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta faru a lardin Sichuan tare da jama'ar duk kasar Sin baki daya.

Babbar girgizar kasar da ta faru a ran 12 ga wata a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan ta yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 32,000 tare da kuma jikkata wasu dubu 220 da ke larduna Sichuan da Gansu da Shanxi da sauran wuraren kasar Sin. Domin bayyana babban alhinin da dukkan jama'ar kasar Sin ke nuna wa mutanen da suka mutu sabo da girgizar kasa, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kuduri cewa, kwanaki 3 wato daga ran 19 zuwa ran 21 ga watan Mayu na wannan shekara za su zama ranakun zaman  makoki a duk kasar Sin. Cikin wannan lokaci, za a dakatar da aikin mika wutar wasannin Olimpic a cikin kasar. Hukumomin duk kasar Sin da wadanda ke kasashen ketare za su saukar da tutocin Sin zura rabin sanda domin nuna alhini, kuma za a tsayar da bukukuwan nishadi na jama'a, kuma an ajiye littattafan rubutu a ma'aikatar harkokin waje na kasar, da ofisoshin jakadanci da na consulate na kasar Sin da ke kasashen waje domin zaman makoki.

Yau da safe a wurare daban-daban na kasar Sin kuma an yi bukin saukar da tutar kasa zuwa rabin sanda domin muna alhini ga mutanen da suka mutu cikin babbar girgizar kasa.


1 2