Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-19 20:49:52    
Ana tabbatar da samar da isashen kayayyaki a kasuwannnin yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan, a cewar ministan kasuwanci na kasar

cri
Kwanan baya, ministan kasuwanci na kasar Sin Chen Deming, ya bayyana a lardin Sichuan cewa, yanzu ana iya samar da isashen kayayyaki a kasuwar kasar Sin, wurare daban daban suna sa himma domin nuna goyon baya ga ayyukan fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan, saboda haka, ana iya ba da tabbaci wajen samar da kayayyaki a kasuwannin yankuna masu fama da bala'in.

Mr. Chen Deming ya yi wannan bayani ne, bayan da ya fahimci halin samar da kayayyaki da ake ciki a kasuwannin yankuna masu fama da bala'in, ciki har da Chengdu, da Mianyang, da dai sauransu.

Mr. Chen Deming ya ce, a wuraren da ake zaunar da mutane masu fama da bala'in, masu ayyukan da abin ya shafa za su yi amfani da gine-gine masu sauki, don ba da hidimar ciniki cikin lokaci. (Bilkisu)