Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-19 17:18:04    
Shugabannin kasar Sin sun yi tsit tare da jama'a 'yan kabilu daban daban na kasar don nuna alhini ga wadanda suka rasa rayukansu a girgizar kasa da ta afkawa garin Wenchuan na kasar

cri
Yau 19 ga wata da yamma, da karfe 2 da minti 28, shugabannin kasar Sin, ciki kuwa har da Hu Jintao da Jiang Zemin da Wu Bangguo da Wen Jiabao da Jia Qinglin da Li Changchun da Xi Jinping da Li Keqiang da He Guoqiang da Zhou Yongkang da dai sauransu, sun yi tsit tare da jama'a 'yan kabilu daban daban na kasar, don nuna alhini da ta'aziyya ga wadanda suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasa mai tsanani da ta auku a gumdumar Wenchuan ta lardin Sichuan da ke kudu masu yammacin kasar Sin.

Yau da sassafe, a filin Tian'anmen da ke nan birnin Beijing, an saukar da tutar kasar Sin zuwa rabin sanda, don nuna alhini sosai ga wadanda suka rasa rayukansu sakamakon girgizar.

A ran 19 ga wata da safe, bi da bi ne jakadun kasashe 80 da ke nan kasar Sin da wakilan kungiyoyin duniya suka tafi ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, don nuna ta'aziyya ga wadanda suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasar.

Har wa yau kuma, a dukan hukumomin gwamnati da makarantu da dai sauran muhimman wurare na Hongkong da Macao, an saukar da tutar kasar Sin zuwa rabin sanda, don nuna ta'aziyya ga wadanda suka riga mu gidan gaskiya sakamakon girgizar. A ran nan da yamma, da karfe 2 da minti 28, kungiyoyin agaji da suka zo daga kasashen Rasha da Koriya ta kudu da Japan da Singapore su ma sun nuna alhini ga wadanda suka mutu a girgizar.

Ya zuwa ran 19 ga wata da safe, sakamakon girgizar kasa mai tsanani da ta afkawa gumdumar Wenchuan, mutane 34073 sun rasa rayukansu, a yayin da wasu sama da dubu 240 suka jikkata.(Lubabatu)