Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-19 17:29:10    
Kasashen duniya da Sinawa da ke zama a kasashen waje da kuma abokai na kasashen waje sun ci gaba da ba da taimako ga yankunan girgizar kasa

cri

Bayan da babbar girgizar kasa ta faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, kasashen duniya sun ci gaba da ba da taimako ga yankunan da ke fama da bala'in, Sinawa da ke zaune a kasashen waje da kuma abokai na kasashen waje sun ba da kyautar kudi ga kasar Sin a 'yan kwanakin baya.

Shugabannin kasashen Afirka ta kudu, da Argentina, da Guyana, da Zimbabuwei, da dai sauransu sun nuna jejeto ga shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao. Firayin ministocin kasashen Malasiya, da Tajikistan, da Faransa, da Sweden, da Masar da dai sauransu sun nuna jejeto ga firayin ministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao.

A sa'i daya kuma, Sinawa da ke zama a kasashen waje, da daliban kasar Sin da ke karatu a ketare, da dai sauransu sun bayar da kyautar kudi ga kasar Sin.

A 'yan kwanakin baya kuma, bi da bi ne, kamfanonin dillancin labaru na kasa da kasa suka bayar da bayanai, inda suka yaba wa gwamnatin kasar Sin da jama'arta wajen gudanar da ayyukan ceto yadda ya kamata, da kuma bayar da labarai a fili.(Danladi)