Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-19 15:11:49    
Bangaren soja na kasar Sin ya yi iyakacin kokarin aiwatar da aikin ceton bala'in girgizar kasar Sin

cri

Bayan aukuwar lamarin girgizar kasa mai tsanani a lardin Sichuan na kasar Sin, rundunar sojojin kasar Sin da rundunar sojoji 'yan sanda na kasar Sin sun yi saurin shiga cikin ayyukan yin ceton bala'in girgizar kasa. Bisa matsayin babban karfi na ba da ceto ga bala'in girgizar kasa, rundunar sojoji da rundunar sojoji 'yan sanda na kasar Sin sun riga sun tura mutane dubu 110 ko fiye zuwa wuraren da suka gamu da bala'in girgizar kasa. Bangaren soja na kasar Sin ya bayyana a ranar 18 ga wannan wata cewa, yanzu, aikin ba da ceto ga bala'in girgizar kasa ya riga ya shiga mataki mai muhimmanci, rundunar sojoji da rundunar sojoji 'yan sanda za su ci gaba da kokarinsu na ceton jama'ar da har wa yau dai suke fama da girgizar kasa, kuma cikin himma da kwazo ne suke ba da taimako ga jama'ar da ke wurin gamu da bala'in don sake gina garinsu da sake farfado da aikin fitar da albarka.

Bayan aukuwar bala'in girgizar kasa a ranar 12 ga wannan wata a kasar Sin, an dauke wutar lantarki da ruwa da sadarwa a wasu manyan wuraren da suke gamu da bala'in girgizar kasa ciki har da garin Wenchuan da ke tsakiyar wuraren da bala'in girgizar kasar ya shafa, saboda haka wuraren sun rasa hanyar yin cudanya tsakaninsu da wuraren da ke waje da su. A sa'i daya kuma, girgizar kasar ta sa wasu jikin duwatsu sun yi gangara kwari, sa'anan kuma yanayin sararin samaniya ya yi maras kyau sosai, har ma ana ci gaba da girgizar kasar, wannan ya kara tsananin mawuyacin hali ga aikin ba da ceto ga bala'in girgizar kasa. Bisa halin nan ne, bangaren soja sun shirya hafshoshi da sojoji da yawa don tinkari zuwa wuraren da ke gamu da bala'in, suna iyakacin kokarinsu na neman hanyoyin ba da ceto ga jama'ar da suke fama da bala'in. A cikin gajeren lokacin da ya kai minti 14 bayan aukuwar girgizar kasar, kungiyar farko ta ba da ceto ga bala'in girgizar kasar ta bangaren soja na kasar Sin ta tashi zuwa wuraren da ke fama da bala'in.


1 2