Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-19 15:02:31    
Bayani game da Cedai Drolma, zabiya 'yar kabilar Tibet

cri

An haifi zabiya Cedai Drolma a shekarar 1937 cikin wani iyalin manoma bayi da ke shiyyar Xigaze ta jiyar Tibet. A cikin harshen kabilar Tibet, kalmar Cedai ma'anarta tsawon rai ne, ma'anar Drolma kuwa mace ce. amma kafin jihar Tibet ta samu 'yancin kanta wato a lokacin da Cedai Drolma take yarinya, ita da 'yan iyalinta sun yi zama cikin talauci, suna tafiyar da zama ne ta hanyar yin kwatago domin masarautan bayi. Ta ce,

"A wancan lokaci iyalina mai talauci ne, ba mu da gonaki da gidaje, dukkan gonaki da gidaje na masarautan bayi ne, sabo da haka mu bayi manoma muna zaman cikin talauci. Mun yi hayar gonaki daga wajen masu arziki, muna aikin gona kuma mun samu girbi, amma mun biya musu bashi da mugun ruwa, ba mu iya samun tabbaci ga zaman rayuwarmu sosai ba".

Bayan da jihar Tibet ta samu 'yancin kanta a shekarar 1959, madam Cedai Drolma ta juya akalarta, wata rana ba zata ta shiga cikin hadaddiyar kungiyar 'yan mata ta jihar Tibet, kuma takan halartar bukukuwan nishadi da nuna wasannin da hadaddiyar kungiyar ta shirya.

Lokacin da madam Cedai Drolma take da shekaru 21 da haihuwa, ta zama wata mawakiya ce mai shahara a wurin da take zama. A shekarar 1958, an shigar da ita cikin jami'ar kade-kade ta birnin Shanghai. Ta bayyana cewa,

"Mutane da yawa dake cikin kungiyar 'yan wasanninmu sun shiga jarrabawa, amma bayan da malaman koyarwa sun ji wakar da na rera, sun ce muryata tana da dadi, shi ya sa sun dauke ni cikin jami'ar"

Mawakiya Cedai Drolma ta shiga cikin jami'ar kade-kade ta birnin Shanghai sakamakon muryar wakokin da ta rera, amma sabo da tsawon lokacin da take karatu cikin makarantar firamare bai kai shekara daya ba, shi ya sa ta fuskanci babban kalubale lokacin da take koyo cikin jami'ar. Ko da yake malaman koyarwa sun yi mata yabo bisa dadin muryarta, amma ba ta iya karatu da rububu ba, kuma ba ta fahimci tsarin kide-kide ba, sabo da haka ta samu ci gaba sannu-sannu wajen karatu, har ma ta yi nufin bar jama'ir, ta ce,

"Da farkon zuwana jami'ar, ba na jin harshen kabilar Han, ina shan wahala wajen koyon fasahar kide-kide a jami'a, shi ya sa ian son in bar jami'ar don komawa gida".

Bayan da aka samu labari game da mawakiya Cedai Drolma, malaman koyarwa na jami'ar sun dauki dararun musamman domin koyar mata fasahar rera wakoki, wato malaminta ya fara koyon harshen kabilar Tibet shi da kansa, kuma dukkan mutane sun mai da ita a matsayin 'yaruwansu, sabo da haka Cedai Drolma ta samu babban ci gaba wajen fasahar rera wakoki. A wannan lokaci kuwa ta dauki nauyin rera wata waka mai suna "'Yantattun manoma bayi suna rera wakoki", wadda aka sanya cikin wata sinima da aka dauka dangane da tarihin jihar Tibet. Ta bayyana cewa,

"Labari game da wannan waka shi ne, ma'aikatar daukan sinima ta Xinyi ta birnin Beijing ta dauki wata gajeriyar sinima a wancan lokaci domin bayyana abubuwan tarihi da rarraba gonaki ga manoma bayi da aka yi a jihar Tibet, a cikin wannan sinima ne aka sanya wakar da na rera mai suna "'Yantattun manoma bayi suna rera wakoki".

Daga baya kuma zabiya Cedai Drolma ta rera wakoki da yawa da harshen kabilar Tibet. Muryarta mai halayen musamman da kaunar-zuci da ta nuna lokacin da take rera waka sun ba mutane zurfaffiyar alama a zukatansu. Waka mai suna "Rera wata wakar tudu domin jam'iyya" da ta "Kan tudun Jinshan na birnin Beijing" da Cedai Drolma ta rera sun zama gama gari a duk kasar Sin baki daya, kuma sun ba da zurfaffiyar alama a zukatan mutane. Domin biyan bukatun samun bunkasuwa a jihar Tibet, bayan da zabiya Cedai Drolma ta samu digirinta daga jami'ar kade-kade ta birnin Shanghai, ta tsaya haikan ta tashi daga birnin, ta koma jihar Tibet wadda take samun bunkasuwa.

Cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce na bayan komawarta jihar Tibet, zabiya Cedai Drolma kullum tana yabawa zaman jin dadin da ake ciki yanzu a jihar Tibet ta hanyar rera wakoki.(Umaru)