Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-19 13:38:06    
Ana cigaba da ba da taimakon kudi da kayayyaki ga wurin da ke fama da bala'in girgizar kasa

cri

Bayan da mummunar girgizar kasa ta faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin a ran 12 ga wata, a cikin kwanakin baya, jama'ar kasar Sin suna cigaba da ba da taimakon kudi da kayayyaki ga wurin da ke fama da bala'in girgizar kasa

Ya zuwa ran 18 ga wata da karfe 12 na tsakiyar rana, yawan taimakon kudin da manyan masana'antun 123 da ke cikin hannun gwamnati suka samar ya kai RMB yuan miliyan 932. darajen kayayyakin da suka samar ya kai RMB yuan miliyan 103.

Ya zuwa ran 18 ga wata da karfe 11 da dare, jama'ar yankin musamman na Hong Kong sun riga sun ba da taimakon kudi na dolar Hong Kong fiye da miliyan 400.

Bala'in girgizar kasa da ya faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan yana jawo hankulan mutanen da ke bin addinin Budda. Ya zuwa yanzu, yawan taimakon kudin da mutanen da ke bin addinin Budda suka samar ya kai kusan RMB yuan dubu 100. ban da haka kuma, bi da bi ne gidajen ibada sun yi bukukuwan Budda domin yin addu'a ga mutanen da suka mutu a sakamakon girgizar kasa.