Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-19 12:27:56    
Kasar Sin ta saukar da tuta zuwa rabin sanda domin nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu a sakamakon bala'in girgizar kasa

cri

Ran 19 ga wata da karfe 4 da minti 58 da safe, bayan da aka daga tuta a filin Tian'anmen da ke birnin Beijing, babban birnin kasar Sin, an saukar da tuta zuwa rabin sanda domin nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu a sakamakon bala'in girgizar kasa da ya faru a lardin Sichuan.

A wannan rana da safe, dukkan manyan wurare ciki har da hukumomin gwamnati da makaranta na yankunan musamman na Hong Kong da Macao sun saukar da tuta zuwa rabin sanda domin nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu.

Mr. Tian Guanghui mazaunan birnin Beijing ya ce, mutane da yawa sun mutu a cikin bala'in girgizar kasa, yana bakin ciki sosai. Kuma wannan shi ne na farko da aka saukar da tuta zuwa rabin sanda domin nuna ta'aziyya ga jama'arta, wannan yana da ban tausayi sosai. Bayan an yi bikin Madam Ma Shufang daga Hong Kong ta ce, jiya da dare ta sami labarin cewa za a saukar da tuta zuwa rabin sanda a filin Tian'anmen, sau yau da sassafe ta je ta wurin domin kallon bikin. Ta ce, dukkan mutanen da suka mutu a sakamakon aukuwar bala'in su ne 'yan uwanmu, muna bakin ciki sosai.

Ya zuwa ran 18 ga wata da karfe 2 na yamma, an riga an tabbatar da mutuwar mutane 32,476, sauran mutane fiye da dubu 220 a lardunan Sichuan, da Gansu, da Shaanxi sun jakkata a sakamakon bala'in girgizar kasa da ya faru a ran 12 ga wannan wata.