Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-19 00:18:56    
(Sabunta) Kasashen duniya suna cigaba da janjantawa, da ba da taimako ga kasar Sin kan bala'in girgizar kasa da aka samu a lardin Sichuan

cri
Bayan da aka samu bala'in girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, tun 'yan kwanakin da suka wuce, kasashen duniya suna cigaba da janjantawa, da ba da taimako ga kasar Sin.

Wadanda suka janjanta shugaba Hu Jintao na kasar Sin su ne: shugaba Thabo Mvuyelwa Mbeki na kasar Afrika ta kudu, da shugaba Cristina Fernandez ta kasar Argentina, da shugaba Bharat Jagdeo na kasar Guyana.

Bayan haka kuma, shugabanni, da kungiyoyi daga kasashen Rasha, da Belorussia, da Kazakhstan, da Faransa, da taron dandalin tattaunawa kan tattalin arziki na duniya, da dai sauransu, sun ma sun janjanta kasar Sin.

A waje daya kuma, kasashen Malaysia, da Australia, da Italy, da sauran kasashe, da kuma kamfannoni da kungiyoyi daga kasashen Japan, da Switzerland sun ba da taimako ta hanyoyi daban daban ga yankunan da ke fama da bala'in na lardin Sichuan.

Bugu da kari kuma, a 'yan kwanakin da suka wuce, ofisoshin jakadanci na kasar Sin da ke kasashen ketare, da 'ya'yan Sinawa mazauna kasashen waje, da hukomomi da kuma daliban kasar Sin da ke kasashen ketare, da dai sauransu, suna cigaba da bayar da taimakon kudi ga lardin Sichuan, don taimakawa mutanen da ke fama da bala'in.

Babban ofishin jakadanci na kasar Sin da ke kasar Nijeriya, ya gabatar da cewa, ya zuwa ranar 17 ga wata, ofishin ya riga ya samu taimakon kudi da yawansu ya kai kudin Sin yuan RMB miliyan 5.2 daga 'ya'yan Sinawa mazauna kasar Nijeriya, da kuma mutane na sada zumunci na kasar.

Kungiyar tarayyar 'ya'yan Sinawa mazauna kasar Kenya, da majalisar tattalin arziki da ciniki ta kasar Sin da ke Kenya sun bayar da sanarwa a ranar 17 ga wata cewa, 'ya'yan Sinawa mazauna kasar, da kuma hukumomi da kamfanonin kasar Sin da ke kasar Kenya sun bayar da taimakon kudi da yawansu ya kai dalar Amurka dubu 101 ga yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa.

Kazalika kuma, 'ya'yan Sinawa mazauna kasashen waje, da hukumomi, da kungiyoyi, da kuma kamfanoni na kasar Sin da ke kasashen ketare, wadanda suka fito daga kasashen Masar, da Amurka, da Philippines, da Japan, da Venezuela, da Belgium, da Burtaniya, da dai sauransu, suna kula da halin fama da bala'in girgizar kasa da ake ciki a nan kasar Sin, a waje daya kuma, suna cigaba da bayar da taimakonsu, don nuna goyon baya ga ayyukan fama da bala'in da na ceto ga kasarsu. (Bilkisu)