Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-16 17:44:11    
Jaridar People's Daily ta ba da sharhin cewa, babu wata wahalar da jama'ar kasar Sin ba za ta iya fuskanta ba

cri
A ran 16 ga wata, jaridar People's Daily ta kasar Sin ta buga wani sharhin cewa, babu wata wahalar da jama'ar kasar Sin ba za ta iya fuskanta ba.

Sharhin ya bayyana cewa, shekara ta 2008 ba wata shekara ta kullum ba ga kasar Sin. A farkon shekarar, an yi kankara mai laushi mai matukar tsanani a kudancin kasar Sin, nan da nan dukkan fadin kasar ta kaddamar da ayyukan fama da bala'in cikin gaggawa, kuma an warware matsalar cikin sauri. A ran 14 ga watan Maris, an ta da manyan mumunan al'amura masu aikata laiffuffuka a birnin Lhasa, hedkwatar jihar Tibet mai cin gashin kai ta kasar Sin. Amma ko wane rukuni ba zai iya tsokanar kudurin dukkan jama'ar kasar Sin wajen kiyaye dinkuwar duk kasa bai daya da hadin kan kabilu ba, shi ya sa jihar Tibet da sauran yankunan kabilar Tibet sun sake samun kwanciyar hankali cikin sauri. Haka kuma wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing ta gamu da cikas daga tsiraran 'yan Tibet masu neman kawo wa kasar Sin baraka yayin da wasu kafofin watsa labaru na yammacin duniya suke jin dadi bisa halin bakin ciki da kasar Sin ke ciki. Amma duk duniya tana jiran gasar wasannin Olympics, da kuma nuna adalci kan batun, Sinawa na duk duniya sun hada kansu sosai.

Ban da wannan kuma sharhin ya ce, an yi girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan ba zato ba tsammani. A ranar aukuwar girgizar kasa, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Hu Jintao ya kira taron zaunannen kwamitin hukumar siyasa da dare domin ba da umurni ga ayyukan ceto. Firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya isa yankuna masu fama da bala'in ba tare da bata lokaci ba, haka kuma sojoji da 'yan sanda fiye da dubu 100 sun shiga yankunan domin ceton mutane. Fararen hula da suke zama a duk fadin kasar Sin, da 'yan uwa na Taiwan da Hong Kong da kuma Macao, da Sinawa 'yan kaka gida na duk duniya suna ta samar da taimakon kudade bisa son ransu.

Bugu da kari kuma sharhin ya nuna cewa, wannan shi ne kasar Sin, jama'ar Sin, gwamnatin Sin, da kuma sojojin kasar Sin. Babu wata wahalar da jama'ar kasar Sin ba za ta iya fuskanta ba.(Kande Gao)