Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-16 17:43:24    
Hu Jintao ya isa yankunan da ke fama da girgizar kasa na lardin Sichuan domin ba da jagoranci ga ayyukan ceto

cri

A ran 16 ga wata da safe, Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasar kuma shugaban kwamitin soja na tsakiya na kasar ya isa yankunan da ke fama da girgizar kasa na lardin Sichuan ta jirgin sama domin nuna jejeto ga fararen hula da shugabannin yankunan, da nuna gaisuwa ga hafsoshi da sojoji da 'yan sanda da kuma masu jiyya da ke gudanar da ayyukan ceto, da kuma ba da jagoranci ga ayyukan fama da bala'in da kuma gudanar da ayyukan ceto.

Shugaba Hu ya jaddada cewa, yanzu aikin fama da girgizar kasa da ceton mutane yana cikin lokaci mafi tsanani. Dole ne a nemi dabaru da kuma haye dukkan wahaloli domin yi iyakacin kokari wajen cimma nasarar wannan yaki.

Haka kuma shugba Hu ya nuna cewa, ko da yake awoyi 72 suka wuce bayan girgizar kasa, amma har yanzu ya kamata a mayar da ayyukan ceton mutane a gaban kome. A waje daya kuma ya kamata a yi wa mutane masu jikkata jiyya, da maido da muhimman ayyukan yau da kullum na zirga-zirga da sadarwa da kuma wutar lantarki, da kuma ba da tabbaci ga zaman fararen hula.(Kande Gao)