Bayan da aka yi mummunar girgizar kasa mai karfin digiri 7.8 na ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin a ran 12 ga wata, a kwanan baya, kasashen duniya sun nuna goyon baya ga kokarin da gwamnatin Sin da jama'ar Sin suke yi wajen fama da girgizar kasar da kuma gudanar ayyukan ceto. Wasu shugabannin kungiyoyin duniya da na yankuna sun nuna yabo ga kasar Sin bisa kyawawan ayyukan ceto da take yi cikin sauri.
A lokacin da yake zantawa da wakilin gidan rediyo na Majalisar Dinkin Duniya, Stephen Martin, wani kwararren hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, wanda yake kula da shirin shawo kan cututtuka da harkokin ba zata na jin kai ya bayyana cewa, gwamnatin Sin tana gudanar da ayyukan ceto cikin sauri yadda ya kamata. Abubuwan da take yi na da matukar muhimmanci wajen rage yiwuwar barkewar cututtuka masu yaduwa.
Sa'an nan kuma, ran 15 ga wata da dare, Jean Ping, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka wato AU ya ba da sanarwar cewa, kwamitin AU ya nuna yabo da goyon baya ga gwamnatin Sin da jama'ar Sin bisa kokarin da suke yi domin fama da girgizar kasa da kuma ayyukan ceto da suke yi a yanzu. Yana fatan wadanda suka jikkata a girgizar kasar za su samu sauki cikin sauri.(Tasallah)
|